✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kayar da ’yan Majalisar Wakilai 2 a Ondo

'Yan majalisar sun nemi yin ta-zarce amma suka sha kaye

Tajudeen Adefisoye (PDP) da Gboluga Ikengboju (APC), ’yan Majalisar Wakilai ne a  Jihar Ondo masu neman ta-zarce a zaben 2023, sai dai baki daya ba su kai bantensu ba.

Tajudeen Adefisoye shi ne dan mai wakiltar mazabar Ifedore/Idanre, sannan Gboluga Ikengboju ke wakiltar Okitipupa/Irele na jihar.

Adefisoye ya sha kaye ne hannun abokin hamayyarsa na PDP, Festus Akingbaso, a zaben da ya gudana ranar Asabar, a yayin da Ikengboju ya sha kaye a hannun Jimi Odimayo.

A cewar INEC, Adefisoye na APC ya samu kuri’u 20,064, sannan abokin hamayyarsa, Akingbaso, ya samu 24,263.

A hannu guda, Odimayo na Jama’iyyar PDP ya tashi da kuri’u 44,638, Ikengboju kuma 21,066.

A ranar Lahadi INEC ta bayyana Adefisoye da Odimayo a matsayin wadanda suka lashe zabe a yankunansu.