✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kayyade farashin takin zamani kan N5,000

Gwamnati ta rage rabin farashin takin Urea, na NPK kuma ya koma N5,000 a Binuwai.

Gwamnati ta kayyade farashin buhun takin zamani a kan Naira 6,000 a daminar bana a Jihar Binuwai.

Da yake kaddamar da sayar da takin zamanin a garin Makurdi, Gwamnan Jihar, Samuel Ortom, ya ce gwamnatinsa ta rage rabin farashin takin Urea domin saukaka wa manoma.

Ya ce yanzu farashin takin Urea zai koma N6,000 daga N12,000, shi kuma NPK daga N9,000 ya koma N5,000.

A cewarsa, gwamnatin ta tattauna da dillalai da za su samar da takin zamani cikin tirela 141 wanda nauyinsa ya kai metric ton 4,380 a bana.

Ya ce a yunkurinta na bunkasa harkar noma, gwamnatin ta raba wa manoma taraktoci 50 a kan farashi mai rahusa.

Ortom ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan taimakon da ta yi wa manoman jihar da ambaliya ta yi wa barna a shekarun 2017 da 2018 ta hanyar ba su takin zamani ta hannun Hukumar ba da Agaji Kasa ta (NEMA).