Harkokin koyo ka koyarwa sun dawo gadan-gadan A Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta Zariya a ranar Talata.
Daliban jami’ar sun koma aji a wannan satin ne kamar yadda jaddawalin shekarar karatu na 2021/2022 da hukumar makarantar ta amince da shi.
- DAGA LARABA: Yadda Yaudara Ta Zamo Ruwan Dare A Fagen Soyayya
- Yadda matar aure ta samu digiri mai daraja ta daya a fannin Lissafi daga Jami’ar ABU
Hakan kuwa na zuwa ne kimanin wata uku tun bayan janye yajin aikin Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) a watan Oktoba, 2022.
Sai dai kuma bincike ya nuna cewa kalilan daga cikin dalibai ne suka dawo makarantar suka fara daukar darussa.
A wani zagayen gani da ido da mahukuntan jami’ar suka gudanar, karkashin jagorancin Shugaban Jami’ar, Farfesa Kabiru Bala, ya bayyana rashin jin dadi bisa karancin dawowar dalibai.
Su ma wasu jami’an jami’ar da suka zagaya sun nuna rashin jin dadinsu bisa rashin dawowar daliban duk kuwa da sanin cewa an fara karatu ka’ina-da-na’in.
Koda yake babu tabbacin ko karancin dawowar daliban na da nasaba da hutun bukukuwan karshen shekara da aka kammala a ranar Litinin.
Duk da haka, a lokacin da wakilinmu ya ziyarci sashen nazarin aikin lauya na jami’ar da ke Kongo, ya tarar dalibai da yawa sun dawo.