✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kona babura 25 bayan da dan acaba ya yi ajalin mace a Legas

'Yan acaban sun gudu ne saboda kada a huce takaici a kansu

Gungun wasu fusatattun matasa a Jihar Legas, sun tattara tare da kona baburan ‘yan acaba guda 25 kurmus bayan wani dan acaba ya yi sanadiyyar mutuwar wata mace a Jihar.

An ce ganin abin da ya faru ne, ya sa ’yan acaban da ke wurin suka tsere suka bar baburansu gudun kada ‘yan daban yankin su sauke fushinsu a kansu, wanda hakan ya bai wa ‘yan daban damar tatattara baburansu suka banka musu wuta.

Hatsarin ya auku ne ranar Alhamis a kan hanyar Jakande/Isheri, inda bisa kuskure dan acaban ya buge marigayiyar da ba a tantance ko wace ce ba, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwarta nan take.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwan haka a shafinsa na Twitter wanda Kamfanin Dilancin Labarai na Najeriya ya bi diddigi. Hundeyin ya ce, dan acaban ya kuskure hanya ne ya buge marigayiyar, kuma nan take rai ya yi halinsa.

“’Yan sanda sun dauki dan acaban zuwa asibiti don yi masa magani, haka ma sun dauke gawar.

“Kafin ‘yan sanda su je su dawo, wasu fusatattu sun tattara baburan da ke wurin sun banka musu wuta, babura 25 suka kona,” inji jami’in.

Daga nan ya ce, Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta yi tir da wannan mummunan hukuncin, tare da cewa za su hukunta duk wanda aka kama yana da hannu cikin badakalar.

(NAN)