✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kona motoci 874 a Faransa saboda murnar sabuwar shekara

A bana dai yawan motocin da aka kona ya ragu in aka kwatanta da a 2019.

A kasar Faransa, an kona akalla motoci 874 a jajiberin sabuwar shekarar 2022, a wata al’adar da aka jima ana sukarta.

Sai dai a bana, adadin ya ragu matuka, in aka kwatanta da guda 1,316 din da aka kona a 2019, kamar yadda Ministan Cikin Gidan Kasar  Gerald Darmanin ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Asabar.

An dai rage yawan motocin ne saboda yawan ’yan sandan da suke kokarin tursasa jama’a bin matakan kariyar COVID-19, sakamakon samfurin Omicron mai saurin yaduwa da ya sake bulla.

Sai dai a bara, babu cikakken adadin motocin da aka kona saboda dokar kullen Corona.

Kamar a kasashe da dama dai, a Faransa ana kone motocin ne saboda masu aikata laifin da ke konawa don su bad-da-sahu da kuma masu yin ikirarin yin inshora na karya.

Sai dai a Faransa, lamarin ya dauki sabon salo, inda ake yi domin bikin sabuwar shekara.

Tarihi ya nuna cewa an fara bikin ne tsakanin matasa a yankin Strasbourg da ke Gabashin kasar a shekarun 1990.

Kazalika, an yi amfani da dabi’ar wajen yin zanga-zangar nuna fushin matasa kan wata dokar gine-gine a kasar a shekarar 2005.

A lokacin dai, ’yan sanda sun kirga kimanin motoci 8,810 da aka kona cikin kasa da mako uku.