✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori karamin Ministan Kudin Ghana saboda cin hanci

Ana zarginsa ne da badakalar hakar zinare a kasar

Shugaban Kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya kori karamin Ministan Kudin kasar, Charles Adu Boahen.

Cikin sanarwar da ta fitar ranar Litinin, Fadar Shugaban Kasar ta ce, ta dauki matakin korar Ministan ne saboda zargin rashawa da ake yi masa da ya shafi hakar ma’adinin zinare a kasar.

Gidan talabijin na Aljazeera ya rawaito cewa, kwannan nan dan jaridar nan mai binciken kwakwaf a kasar, Anas Aremeyaw Anas ya yi zargin Boahen ya karbi cin hanci daga hannun ’yan kasuwa don ba su damar hako zinare a kasar.

Sanarwar ta kara da cewa tuni Shugaba Akufo-Addo ya mika batun ga sashen tuhuma don gudanar da bincike.

Hakar ma’adinai sana’a ce babba a kasar Ghana, kasa ta biyu mafi arzikin zinare a nahiyar Afirka.

A hannu guda, shi ma babban Ministan Kudi na Ghana, Ken Ofori-Atta na fuskantar kiraye-kiraye kan a tsige shi saboda zargin rashawa da ake yi masa na tafiyar da tattalin arzikin kasar ba yadda ya kamata ba.

A ranar shida ga watan Nuwamban 2022, daruruwan masu zanga-anga suka yi dafifi a Accra babban birnin kasar, inda suka yi kira ga Shugaba Nana Akufo-Addo ya yi murabus saboda matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta a karkashin gwamnatinsa.