✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori sanatan da bai taba halartar zaman majalisa ba

Rashin halartarsa zaman majalisar ya tunzura sanatoci.

’Yan majalisar Japan sun kori wani sanata daga Majalisar Dattawan kasar bayan ya kwashe wata bakwai bai halarci zaman majalisar ba.

Sanatan – wanda fitacccen mai amfani da shafin YouTube ne – ya zama dan majalisa na farko da aka kora ba tare da ya taba shiga zauren Majalisar Dattawan ba tun da aka zabe shi.

Sanatocin sun kori Sanata Yoshikazu Higashitani ne a ranar Talata sakamakon rashin halartar zaman majalisar.

Tunda aka zabe shi wata bakwai da suka gabata, ko sau daya bai taba halartar zaman majalisar ba, kamar yadda kafar labarai ta BBC ta ruwaito.

Kwamitin Ladabtarwa na majalisar ne ya yanke hukunci korarsa saboda ci gaba da kin halartar zaman majalisar da yake yi.

Sanata Yoshikazu Higashitani

A watan Yulin bara aka zabi Mista Higashitani a majalisar, kuma sanatan – wanda aka fi sani da ‘GaaSyy’ a shafin YouTube ya yi fice wajen wallafa shahararrun bidiyoyinsa – ya zama sanata na farko da aka taba kora bisa laifin kin halartar majalisa.

Hukuncin kora shi ne hukunci mafi tsauri da dan majalisa zai fuskanta. Kuma a tarihin kasar wannan ne karo na biyu da hakan ta taba faruwa tun 1950.

Nan gaba kadan ne a makon nan majalisar za ta tabbatar da korar sanatan a hukumance.

Rahotonni sun ce sanatan na zaune ne a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Kafofin yada labaran Japan sun ce sanatan ya ki halartar zaman majalisar ce sakamakon fargabar kama shi bisa zargin aikata laifin zamba da bata suna da wasu shahararrun mutane ke yi masa.

Yana daya daga cikin zababbun ’yan majalisa biyu daga jam’iyyar hamayya ta NHK, jam’iyya daya tilo da ke kirayekirayen sauya bangaren yada labaran kasar.

Jaridar Asahi Shimbun ta ce jam’iyyar na yawan sauya sunanta saboda dalilai na neman shahara.

Bijirewa kiran ‘yan majalisar

A makon jiya, Majalisar Dattawan ta nemi Mista Higashitani ya je birnin Tokyo domin neman afuwa a zauren majalisar kan kin halartar zaman majalisar da ya yi.

‘Yan majalisar sun ce wannan ita ce dama ta karshe da za su bai wa sanatan domin ci gaba da kasancewa mamba a majalisar.

Sai dai Mista Higashitani ya ki yarda ya halarci zaman majalisar, kamar yadda abokan aikinsa suka bukata.

Maimakon haka, sai ya bayyana a shafinsa na YouTube cewa zai tafi kasar Turkiyya.

Kuma ya ce yana shirin sadaukar da albashinsa domin tallafa wa mutanen da bala’in girgizar kasar Turkiyya ta shafa.

Rashin halartarsa zaman majalisar ya tunzura sanatocin – wadanda suka amince da kada kuri’ar korarsa a wannan mako.

Dan majalisa daya tilo da ke jam’iyya daya da sanatan, Hamada Satoshi, ya ce korar sanatan da aka yi bisa laifin rashin halartar majalisar ba ya kan tsarin doka.