✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kori shugabannin kamfanin wutar lantarkin Abuja kan dauke wuta

Ma'aikata sun shiga yajin aiki kan rashin biyan su albashi da alawus-alawus

Shugaba Muhammadu Buhari ya kori shugabannin kamfanin wutar lantarki na Abuja (AEDC).

An sallami shugabannin kamfanin ne bayan yajin aikin da ma’aikatan kamfanin suka shiga, wanda ya jefa yankuna da dama a Abuja da jihohin Nasarawa da Neja da Kogi a cikin duhu.

Ma’aikatan sun shiga yajin aikin ne saboda rashin biyan su albashi da alawus-alawus gami da rashin tura kudaden fanshonsu da ake cira daga albashinsu zuwa kamfanonin fansho.

Tuni dai aka cimma yarjejeniya tsakanin bangaren gwamnati da Kungiyar Ma’aikatan Wutar Lantarki ta Kasa (NUEE) reshen Abuja, kan su janye yajin aikin, kuma a biya su duk hakkokinsu cikin kwanan 21.

Da take sanar da korar a ranar Talata, Ma’aikatar Wutar Lantarki ta Tarayya ta ce Shugaba Buhari ya kuma sa a kafa kwamitin gudanarwa na wucin gadi domin ci gaba da tafiyar da al’amuran kafmin.

Sanarwar da kakakin ma’aikatar, Goddy Agba, ya fitar ta ce, “Shugaban Kasa ya kuma umarci Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnat (BPE) ta kafa sabon kwamitin gudanarwar AEDC” inji sanarwar.