✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori sojojin da ake zargi da kisan Sheikh Aisami daga aiki

Lallai a hukunta sojan da ya kashe Sheikh Goni a cewar Shugaba Buhari.

Rundunar sojin Najeriya ta kori dakarunta biyu daga aiki wadanda ake zargi da kisan malamin nan na Jihar Yobe, Sheikh Goni Aisami a makon da ya gabata.

Sojojin biyu, kofur John Gabriel da Adamu Gideon, wadanda rundunar ’yan sandan Najeriya ta gabatar ga manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, inda babban wanda ake zargin ya bayyana yadda ya harbe malamin.

Mukaddashin kwamandan rundunar 241 Reece da ke Nguru na Jihar Yobe, Laftanar Kanar Ibrahim Osabo, ya fada wa manema labarai cewa wani kwamatin hadin gwiwa ne da aka kafa tsakanin ‘yan sanda da sojoji ya kama su da laifin.

BBC ya ruwaito Laftanar Kanar Osabo yana cewa an kori sojojin ne kan tuhuma biyu da suka kunshi gazawa wajen gudanar da aikinsu da kuma bata sunan aikinsu.

Kanar Osabo ya kara da cewa za a mika su ga ‘yan sanda a birnin Damaturu don gurfanar da su a gaban kotu.

Kisan Goni Aisami ya jawo ta da jijiyoyin wuya daga ‘yan Najeriya da shugabanni, inda aka rika kiran yi masa adalci da kuma hukunta waɗanda ake zargin da gaggawa.

Lallai a hukunta sojan da ya kashe Sheikh Goni —Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a hukunta jami’in sojan da ake zargi da kashe Sheikh Goni Aisami bayan malamin ya rage masa hanya a motarsa a Jihar Yobe.

A sakon ta’aziyyarsa ga iyalan mamacin da Gwamnatin Jihar Yobe, Shugaba Buhari ya umarci hukumomin soji su tabbatar da cewa, jami’in da duk wadanda suka taimaka masa sun girbi abin da suka shuka gami da kakkabe duk wani baragurbi a cikin sojojin.

Sanarwar da hadimin Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar ta ce: “Irin wannan kidahumanci na kashe mutum mai tausayi da sojan ya yi, ya saba duk wata koyarwa da kuma horon da aka san soja da shi.”

A cewarsa, an san soja da bin doka da mutunci da kuma sanin martabar rayukan mutane.

“Horon da ake mana a matsayin sojoji shi ne na mu zama masu kamun kai da hakuri da kuma bin doka sau- da-kafa.

“Ba koyarwar soja ba ce cutar da mutane. Abin da wannan sojan ya aikata bakon abu ne, sannan yana barazana ga martabar Rundunar Sojin Kasar nan,” inji Buhari.

Shugaban Kasar ya kara da cewa, “Kisan Sheikh Goni Aisami da sojan ya yi zai iya sa al’ummar kasar nan su razana da sojojinmu, wanda hakan ka iya wargaza yardar da suka yi musu.”

Buni ya dauki ’ya’yan Sheikh Aisami aiki

Tuni dai Gwamnan Jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni ya ba da umarnin a dauki ’ya’yan malamin maza biyu aiki nan take.

Gwamna Buni ya bayar da umarnin ne a lokacin da iyalan Sheikh Goni Aisami suka kai masa ziyarar godiya bisa yadda ya nuna musu kulawa bayan kisan malamin.

Gwamnan, ta bakin Kakakinsa Mamman Muhammad ya ce, gwamnatin jihar za ta gudanar da bincike domin gano hakikanin abin da ya kai ga kashe malamin kuma za ta ci gaba da kulawa da iyalansa.

Malam Ibrahim Aisami, wanda ya yi jawabi a madadin iyalan mamacin, ya ce aikin da Gwamnan ya bai wa ’ya’yan malamin zai taimaka wajen rage kuncin rayuwar da rasuwar mahaifin nasu za ta haifar.