✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori tsohon shugaban Majalisar Filato saboda komawa PDP

Majalisar Dokokin Jihar Filato, ta sanar da korar tsohon Shugaban majalisar mai wakiltar mazabar Jos ta Gabas, Honarabul Ayuba Abok saboda sauya sheka da ya…

Majalisar Dokokin Jihar Filato, ta sanar da korar tsohon Shugaban majalisar mai wakiltar mazabar Jos ta Gabas, Honarabul Ayuba Abok saboda sauya sheka da ya yi daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Majalisar ta sanar da daukar wannan mataki ne a zaman da ta yi a garin Jos, babban birnin Jihar Filato a karkashin jagorancin shugaban majalisar, Honarabul Yakubu Sanda.

Hakan dai na zuwa ne biyo bayan wasikar da majalisar ta samu daga jam’iyyar APC reshen Jihar Filato wadda ta bukaci majalisar ta kori tsohon shugaban majalisar.

A cikin wasikar, APC ta bayyana fushinta dangane da sauya shekara da Honarabul Abok ya yi daga jam’iyyar zuwa PDP, wanda a cewarta hakan ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya sashi na 109 sakin layi na 1.

Aminiya ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata ne tsohon shugaban majalisar, Honarabul Ayuba Abok ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.