✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kubutar da mutum 5 daga masu garkuwa a Kaduna

An kama dillalin makaman 'yan bindiga a Jihar Kaduna

Mutum biyar sun tsallake rijiya da baya hannun masu satar mutane da suka nemi yin garkuwa da su a Birnin Gwari, Jihar Kaduna.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Kaduna, ASP Mohamed Jalige ya ce uku daga cikin wadanda aka kubutar din kananan yara ne.

Ya ce, “Mun samu rahoton ’yan bindiga kusan 10 dauke da muggan makamai sun tare hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari suna neman yin garkuwa da mutum biyar da ke cikin motar da ke hanyar zuwa Birnin Gwari daga Kaduna.

“Jami’anmu da ke Buruku nan take suka kai dauki, suka yi musayar wuta tare da fatattakar maharan zuwa cikin daji bayan sun yi musu raunin bindiga, suka kuma kubutar da mutanen cikin motar.

“Ana ci gaba da kokarin ganin an kamo maharan, tare da mika wadanda aka kubutar da ga iyalansu.”

An kama dillalin makaman ’yan bindigar Kaduna

Kazalika jami’an tsaro sun cafke wani dillalin makamai ’yan bindiga a Jihar Kaduna, suka kuma hallaka wani dan bindiga.

Rundunar ta ce jami’an tsaron rundunar hadin gwiwa ta Operation Yaki ne suka aika dan bindigar lahira.

“A lokacin bin sawun wanda ake zargin mun kwace wata mota kirar Toyota Highlander a Saminaka, Karamar Hukumar Lere.

“Da ganin jami’an tsaro sai ’yan cikin motar suka fara harbin su, su kuma suka mayar da martani suka harbi mutum biyun da ke cikin motar ’yan Jihar Filato, ” inji sanarwar.