✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kulle kamfanoni 2 a Kano saboda karya dokar tsaftar muhalli

Masana’antun da lamarin ya shafa sune kanfanonin robobi na NINA da Prosper Plastic

Kotun tafi-da-gidan-ka kan kare tsaftar muhalli a Jihar Kano ta rufe wasu masana’antu biyu saboda karya dokar tsaftar muhalli wacce ake gudanarwa a kowacce Asabar din karshen wata a jihar.

Masana’antun da lamarin ya shafa su ne kanfanonin robobi na NINA da Prosper Plastic, kuma an umarci kowannen su ya biya tarar N500,000.

A duk ranara tsaftar muhallin dai, akan bukaci dukkan wuraren kasuwanci, kasuwanni da masana’antu su kasance a rufe har zuwa karfe 10:00 na safe.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Auwal Yusuf Suleiman shi ne ya yanke hukuncin yayin duba yadda aikin ya gudana a unguwar masana’antu ta Challawa da ke Kano ranar Asabar.

Alkalin ya ce masana’antun sun karya tanade-tanaden sassa na 61 da na 104 na Kundin Dokokin Tsaftar Muhalli na kasa.

“Za mu bar kamfanonin su sake budewa ne kawai idan suka gabatar da rubutacciyar shaida daga Ma’aikatar Muhalli,” inji shi.

Shi ma da yake tsokaci, Kwamshinan Muhalli na Jihar, Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce kamfanonin ba sa cikin wadanda aka tsame daga tsaftar muhallin saboda yanayin ayyukansu.

Ya kuma yaba wa Hukumar Kula da Hanyoyi da Ababen Hawa ta Jihar (KAROTA) saboda irin gudunmawar da jami’anta suke bayarwa wurin tabbatar da bin dokar.

Kazalika, kotun tafi-da-gidanka din ta yanke wa wasu akalla mutum 10 masu ababen hawa hukunci saboda aikata makamantan wadannan laifukan.