✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwace gurbatatttun magungunan N200m a Kano

An kama masu sauya wa magungunan da suka lalace mazubai don sake sayarwa.

Hukumar Kare Hakkin Kwastomomi ta Jihar Kano (KSCPC) ta kwace jabun magunguna da wadanda suka gurbace na Naira miliyan  200 a cikin wani gini a jihar. 

Manajan-Darakatan KSCPC, Baffa Babba Danagundi ya ce da aka kama ba su da rajista da Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC).

Baya ga haka tawagar da ta kai samamen ta kama bata garin suna sauya wa magungunan da suka daina aiki mazubai da nufin sake fitar da su domin sayarwa a kasuwanni.

Baffa Babba Danagundi ya ce KSCPC ta yi kamen ne a samamen da ta kai bayan samun bayanan sirri kan ayyukan miyagun a wani gini da suke ajiye magungunan suke kuma sauya musu mazubai.

Ya ce a lokacin da aka kai wa ginin da ke layin Niger Street a garin Kano samame, Hukumar ta yi arba da bata garin suna tsaka da aikata mummunan aikin a cikin ginin.