✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwakule idon wani karamin yaro a Bauchi

Wani wanda ya san yaron ne ya kai shi gona ya daure shi sannan ya kwakule mishi idanu.

An kwakule idon wani karamin yaro mai shekara 16 a Kwanan Gulmanmu da ke Unguwar Jahun a cikin garin Bauchi.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Bauchi, Umar Mamman Sanda, ne ya bayyana hakan a wata takardar manema labarai mai dauke da sa hannun Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, SP Mohammed Ahmed Wakil da cewa Kwamishinan ya sha alwashin gano tushen lamarin.

“Wanda abin ya shafa ya bayyana cewa, wani Ibrahim na Rafin Zurfi wanda ya san shi da dadewa ya kai shi daji don yi mishi aika-aika a gonarsa, inda ya yi amfani da wayar igiyar ruwa ya daure shi da karfi kafin ya cire idanunsa biyu,” inji shi.

Kwamishinan ya ce a halin yanzu wanda abin ya shafa yana kwance a asibiti ana kula da lafiyarsa, yayin da ake gudanar da bincike.

Sanda ya ce ’yan sanda za su tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su zama abin izna don hana maimatuwar hakan a nan gaba.

Ya ce “Da misalin karfe 6:00 na safe ne Mai Unguwar Birshi, Mohammed Lawal ya shaida wa ’yan sanda cewa an gano wani yaro dan kimanin shekara 16 a cikin jininsa tare da an cire masa idanu biyu.

“An gano yaron ne a dutsen Jira na unguwar Yelwa, cikin garin Bauchi.

“Tawagar ’yan sanda karkashin jagorancin DPO na Yelwa sun je wurin da abin ya faru, inda suka dauki yaron zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi (ATBUTH) domin yi masa magani”.

Kwamishinan ya ce, “Bincike na farko ya nuna sunan wanda aka cire wa idon Uzairu Salisu yana Kwanan Gulmammu unguwar Jahun.”

Sanda ya bayyana cewa a halin yanzu wanda abin ya shafa yana kwance a asibiti ana kula da lafiyarsa, yayin da ake gudanar da bincike.

Ya sake nanata bukatar iyaye da masu kula da yara su rika sanya ido sosai kan abubuwan da ke ke faruwa a unguwanninsu.

Ya kuma yi kira ga shugabannin al’umma, dattawa da masu mulki da su masu lura da abubuwan da ke faruwa a yankunansu tare da tabbatar da sa baki kafin al’amura su lalace.

Sanda ya bukaci al’ummar jihar da kada su yi kasa a gwiwa wajen hada kai da ’yan sanda, musamman wajen bayar da bayanai da kuma lura, sannan su kai rahoton duk wani mai aikata laifi ga ’yan sanda.