✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwaso ‘yan Najeriya 4,984 da suka makale a Dubai

Zuwa yanzu ‘yan Najeriya 4,984 aka dawo da su gida bayan sun makale a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), sakamakon bullar Annobar coronavirus.…

Zuwa yanzu ‘yan Najeriya 4,984 aka dawo da su gida bayan sun makale a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), sakamakon bullar Annobar coronavirus.

Galibinsu wadanda suka makalake a kasar sun tsinci kansu a halin ne sakamakon rufe zirga-zirgar jirage tsakanin kasashe domin takaita yaduwar cutar ta coronavirus.

Hukumar Kula da ‘Yan Najeriya da ke Kasashen Waje (NIDCOM) ta wallafa a shafinta na Twitter cewa, “Yanzu an yi sawun jirgi 18 ke nan da suka kwaso ‘yan Najeriya 4,984 daga Dubai. Daga ciki Gwamnatin UAE ta biya wa mutum 517 a jirage uku na kamfanin Fly Dubai da wasu 380 a jirgin Emirates Airline”,

Mutum 252 ne daga cikinsu suka iso Najeriya a ranar Asabar inda aka sauke su a Filin Jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas.

180 daga cikin wadanda suka dawo gwamnatin UAE ce ta biya musu kudin jirgi, saboda rashin kudi a cewar NIDCOM.

Gwamnatin UAE ta ba ‘yan Najeriya da bizarsu ta zama a kasar ta kare wa’adin 17 ga watan Agusta su baro kasarta.

Bayan nan ne Gwamnatin Najeriya ta fara yunkuri tun a makon jiya na ganin ta kwaso su.

NIDCOM ta ce karin ‘yan Najeriya 174 za su baro Dubai a ranar 25 ga Agusta ta jirgin Fly Dubai wanda gwamnatin UAE ta dauki nauyi.

Hakan ya kai adadin ‘yan Najeriya da kasar ta biya wa kudin tikitin jirgi zuwa 1,071 daga Dubai.

A kwanakin baya Shugabar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa ta bukaci ‘yan Najeriyan da suka makale a Dubai da su yi amfani da damar kwaso sun, su dawo gida.