✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kwato makamai fiye da dubu 10 sa’o’i kafin zabe

Yadda makaman ke kwarorowar shi ne babban abin damuwa.

Cibiyar Yaki da Yaduwar Kanana da Manyan Makamai Najeriya (NCCSALW) ta sanar da samun nasarar kwace makamai sama da dubu 10 daga ’yan daba da ’yan ta’adda.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ya rage sa’o’i kalilan ’yan Najeriya su fita rumfunar zabe a ranar Asabar domin kada kuri’unsu na zaben Shugaban Kasa da ’yan Majalisar Tarayya.

Shugaban wannan cibiya, Manjo Janar Abba Dikko ya shaida wa manema labarai a Maiduguri cewa sun kwato dubban makamai kala-kala a hannun ‘yan daba da ‘yan ta’adda da zummar samar da yanayi da za a yi zabe ba tare da tashin hankali ba.

A cewar Manjon-Janar Dikko, “Ba kwato wadannan makamai ba toshe hanyoyin da ake shigo da su shi ne aka fi nuna damuwa.”

Sai dai masana tsaro da su ka jinjinawa wannan cibiya bisa wannan nasarar, sun ce hakan bai isa ba sai an kara daukar matakai na dakile dukkanin hanyoyin shigowa da makamai da ma yaduwarsu a cikin kasa da kan iyakokin kasa.

Matsalar yaduwar haramtattun kanana da manyan makamai tsakanin wadanda da ba su da hurumin rikesu ta jima ta na ci wa hukumomi tuwo a kwarya wanda ake ganin sune ke ruruta wutar rikici da kuma karfafa ayyukan ’yan ta’adda a Najeriya da kasashe makobta.

Wannan ne ya sa cibiyar yaki da yaduwar kanana da manyan makamai ta Najeriya ta mayar da hankali wajen zakulo irin wadannan makamai da ake amfani da su wajen tayar da hankulan musamman a wannan lokaci da ake shirin yin zabe.