✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An lakada wa dan majalisa duka a rikicin shugabanci

An ba hamata iska a rikicin shugabancin Majalisar Jihar Kaduna da ya sa wani mamba yunkurin dauke sandar majalisar. Rikici ya barke ne bayan ’yan…

An ba hamata iska a rikicin shugabancin Majalisar Jihar Kaduna da ya sa wani mamba yunkurin dauke sandar majalisar.

Rikici ya barke ne bayan ’yan majalisa 24 cikin 34 sun tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Muktar Hazo daga kujerarsa a zaman gaggawa da Akawun Majalisar Bello Idris ya jagoranta ranar Alhamis.

Bello Idris ya ce ‘yan majalisar sun maye gurbin Honorabul Hazo ne da Honorabul Iseac Auta Zankai.

Tsigewar ta biyo bayan zargin yunkurin tsige Shugaban Majalisar Yusuf Ibrahim Zailani da Muktar Hazo da wasu mambobi suka yi amma hakan bai yiwu ba.

Jim kadan da tsige shi ne Muktar Hazo da wasu ’yan majalisar magoya bayansa suka shigo harabar a fusace.

Ana cikin haka ne Dan Majalisa Mai wakiltar Makera Dahiru Liman ya dauke sandar majalisar da nufin ficewa da ita domin nuna rashin amincewarsu da zaman da ake yi.

Kafin ficewarsa daga zauren majalisar ’yan majalisar masu goyon bayan Zailani suka rufe shi suka yi ta masa luguden naushi.

Da kyar aka kwaci Dahiru Liman —wanda ya makalkale sandar majalisar, da kayansa a yayyage hancinsa kuma jina-jina.

Da yake bayani ga manema labarai Liman ya ce suna neman tsige Zailani ne saboda rashin kwarewa da raba kawunan ’yan majalisar da yake yi sannan kuma ya ki kiran a zauna a majalisa.

Shugaban Majalisar ya karyata zargin inda ya ce ba su zama a majalisa ne saboda cutar coronavirus da ta sa aka rufe wurare.

Ya kuma musanta zargin da ake masa na raba kawunan ‘yan majalisar wadanda ya ce bai dade da fara shugabanta ba.