✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An gurfanar da dan ‘Adaidaita Sahu’ a gaban Kotu kan zargin damfara

An gurfanar da wani matashi mai shekaru 18 a gaban wata Kotun Majistire da ke zamanta a Kano, kan zargin neman yin sama da fadin…

An gurfanar da wani matashi mai shekaru 18 a gaban wata Kotun Majistire da ke zamanta a Kano, kan zargin neman yin sama da fadin wani baburin Adaidaita Sahu kwana daya da bashi ya rika sojan haya.

Matashin wanda mazaunin unguwar Rimin Auzinawa ce da ke birnin Kano, ana tuhumarsa da aikata laifuka biyu da suka hada rashin gaskiya da zamba cikin aminci, wanda hakan ya saba da sashe na 312 da 322 na kundin dokokin manyan laifuka.

Dan sanda mai shigar da kara Sufeta Umar Tahir, ya shaida wa kotun cewa, wani mai suna Aminu Abdulkadir, mazaunin Karamar Hukumar Rimin Gado ta Jihar ne ya shigar da korafinsa a Ofishin ‘Yan sanda da ke unguwar Rijiyar Zaki a ranar 28, ga watan Febarairun 2021 kan batun.

Ya ci gaba da bayyana wa Kotun cewa, da misalin karfe 7:00 na safiyar ranar 27 ga watan Fabarairun 2021, wanda ake tuhumar ya je wajen ya samu Aminu da bukatar ya bashi baburin ya rika masa sojan hayan yana kawo masa kudi a kullum.

Tahir ya ce, bayan Aminu ya bashi babur din mai lamba RNG405VL wanda darajarsa ta kai  Naira 710,000, sai kwatsam bayan kwana daya ya dawo ya ce barayi sun sace shi.

Dan sandan ya kara da cewa, shi kuwa wanda ake tuhumar ya kafe a kan cewa sace babur din aka yi bayan ya ajiye shi a unguwar Rimin Auzinawa da ke Kano.

Sufeta Tahir ya bukaci kotun  ta dage sauraren karar don ba wa Jami’an ‘yan sanda cikakkiyar damar zurfafa bincike kan lamarin.

Alkalin Kotun, Malam Musa Ibrahim, ya bayar da belin wanda tuhuma kan kudi N50,000 da mutane biyu da za su tsaya masa kan karar kuma daya daga cikin wadanda za su tsaya masa wajibi ne ya zama shugaban Kungiyar matuka babura mai kafa uku ko Sakatarensa, dayan kuma ya zama Dan uwa shakiki.

A karshe Alkali Ibrahim, ya dage zaman sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Maris na shekarar 2021.