✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An mayar da mu saniyar ware a harkar titin jirgin kasa –Gwamnan Gombe

Gwamnan ya koka matuka kan yadda ya ce an yi shakulatin-bangaro da yankin a ayyukan titin jirgin kasan.

Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya ya zargi Gwamnatin Tarayya da mayar da yankin Arewa maso Gabas saniyar ware a ayyukan titin jirgin kasa da take yi a sassa daban-daban na Najeriya.

Ya bayyana hakan ne ranar Alhamis lokacin da Minista a Ma’aikatar Sufuri, Sanata Gbemisola Saraki ta ziyarce shi a fadar gwamnatin jihar dake Gombe.

Ya koka kan yadda ya ce an yi shakulatin-bangaro da aikin shiyyar Gabashin Najeriya wanda ya hada Maiduguri da Gombe da Fatakwal, duk kuwa da irin muhimmancinsa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa.

A cewar Gwamna Inuwa, “Yankin Arewa maso Gabas shine wanda Ma’aikatar Sufuri ta fi mayarwa saniyar ware. Saboda haka, a matsayinki na Minista a ma’aikatar, ya zama wajibi ki sake duba lamarin.

“Muddin za a kai layin dogo har zuwa Jamhuriyar Nijar, ban ga dalilin da zai hana mu ma a yi mana ba.

“Saboda haka muna kira ga Gwamantin Tarayya da ta gaggauta farfado da aiki titin jirgin kasa na shiyyar Fatakwal zuwa Gombe zuwa Maiduguri domin bunkasa tattalin arzikin yankin a kuma saukaka musu hanyoyin sufuri,” inji Gwamnan.

Ya kuma yabawa Gwamnatin kan kafa Cibiyar Harkokin Sufuri ta Najeriya (NITT) a Gombe, wacce ya ce za ta taimaka matuka wajen koyar da sana’o’i ga matasa a jihar, inda ya yi alkawarin daukar nauyin matasa don yin karatu a cibiyar.

Tun da farko dai Minista Gbemisola ta ce ta je jihar ne da nufin kaddamar da reshen cibiyar ta NITT dake garin Kumo a Karamar Hukumar Akko a jihar.

Ta ce cibiyar za ta rika koyar da darussa da za su kai ga bayar da takardar shaidar karama da kuma babbar Diploma a bangaren harkokin sufuri.