✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An mayar da ’yan Arewa 42 gida daga Ondo

An dai tisa keyar matasan ne zuwa jihohin Kano da Jigawa wadanda jihar ta ce galibnsu daga nan suka fito.

Akalla matasa 42 da suka sauka a garin Okitipupa na jihar Ondo daga jihohi daban-daban na Arewacin Najeriya a makon da ya gabata ne aka tisa keyarsu zuwa jihohinsu na asali.

A cewar Gwamnatin Jihar, ta dauki matakin ne saboda suna kawo mata barazanar tsaro.

Dakarun rundunar tsaro ta Amotekun ne dai suka yi wa matasan rakiya dauke da jakunkunansu har suka fice daga cikinta.

Kwamandan rundunar ta Amotekun a jihar ta Ondo, Cif Adetunji Adeleye ya ce sun dauki matakin ne don kare muradun al’ummar jihar.

An dai tisa keyar matasan ne zuwa jihohin Kano da Jigawa wadanda jihar ta ce galibnsu daga nan suka fito.

Da yake gabatar da matasan a Akure, babban birnin jihar, kwamandan ya ce matasan sun yi ikirarin sun zo jihar ne domin koyon aiki a wani kamfanin samar da tsaro mai zaman kansa.

Sai dai ya ce sam ba su gamsu da bayanan matasan ba, inda ya ce yadda suka zo a kan manyan motoci ya tsorata jama’a matuka.

Bugu da kari, Kwamishinan Watsa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Jihar, Donald Ojogo ya ce jihar ta yanke shawarar mayar da su ne don tabbatar da sun isa gida lafiya.