✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An mika wa Abdullahi Abbas shaidar shugabancin APC a Kano

Haruna Danzago ya ce zai daukaka kara kan hukuncin da kotu ta zartar.

Hedikwatar jam’iyyar APC mai mulki, ta mika takardar shaidar shugabancin jam’iyyar ga bangaren Gwamnan Jihar Kano, wanda ya zabi Abdullahi Abbas a matsayin sabon shugaba.

BBC ya ruwaito cewa a yammacin ranar Alhamis ne Sakataren Rikon Jam’iyyar na Kasa, Mista John Akpanudoedehe, ya mika takardar ga Abdullahi Abbas, wanda yake tare da Gwamna Ganduje da dan Majalisar Tarayya Alhassan Ado Doguwa da Kwamishinan Kananan Hukumomi, Murtala Sule Garo.

Bayar da takardar shaidar ta biyo bayan hukuncin da Kotun Daukaka Kara karkashin jagorancin Alkalai uku — Haruna Tsammani, B. I. Gafai da J. Amadi — ta yi ne inda ta soke hukuncin babbar kotun da a baya ta ba bangaren tsohon Gwamnan Jihar Mallam Ibrahim Shekarau nasara a shari’ar shugabancin.

Tuni dai tsagin jam’iyyar APC a Jihar Kano da ke rikici da na Gwamna Abdullahi Ganduje ya ce zai daukaka kara kan hukuncin kotu da ya ce shugabancin bangaren gwamna ne halastacce.

Shugaban tsagin, Ahmadu Haruna Zago, wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Sanata Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa za su yi biyayya ga hukuncin amma za su daukaka kara.

“Za mu daukaka kara mana, ai bin umarnin daban kuma daukaka kara daban,” in ji shi.

“A halin yanzu lauyoyinmu na nazari kan hukuncin kotun.”

Hakan na nufin Kotun Koli ce za ta raba gardama idan suka daukaka karar, kasancewar Kotun Daukaka Kara ce ta yi hukuncin na yanzu.

Aminiya ta ruwaito cewa, a zaman da ta yi ranar Alhamis a Abuja, Kotun Daukaka Kara ta ce Babbar Kotun Abuja ba ta da hurumin yin hukunci kan rikicin sannan kuma ta ce shugabancin Abdullahi Abbas ne halastacce – ba na Haruna Zago ba.

A makon da ya gabata ne tsagin Shekarau ya yi watsi da wani yunkurin sulhu da jam’iyyar ta kasa ta yi, inda ta nada Gwamna Ganduje a matsayin jagoran kwamitin sasanta rikicin da suke yi.

Hukuncin da Kotun ta zartar zai kara hada kawunanmu —Ganduje

Sa’o’i kadan bayan hukuncin da Kotun Daukaka Karar ta zartar, Gwamna Abdullahi Ganduje ya nemi tsagin na tsohon Gwamnan Jihar da ya zo a hada hannu domin ciyar da jam’iyyar APC gaba a Jihar Kano.

Da yake martani kan hukuncin da kotun ta zartar, Gwamnan ya ce tun gabanin soma shari’ar ba ya da wani shakku a kai domin kuwa yana da tabbacin cewa kotun za ta yi abin da ya dace, kuma a yanzu yana farin ciki da hakan.

Gwamnan wanda ya yi wannan furuci ta bakin Kwamishinan Labarai na Jihar Kano, Malam Muhammad Garba, ya ce hukuncin da kotun ta zartar zai kara bunkasa hadin kai da daidaito a jam’iyyar APC reshen Jihar Kano.

A kan haka ne yake cewa yana fatan bangaren Shekarau zai karbi hukuncin da kotun ta zartar a matsayin kaddara ta dawowa a hadu kai da fata domin fasalta jam’iyyar APC a kan turbar da za ta kai kan tudun mun tsira a Zaben 2023 da ke tafe.