✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Mika ’Yan Matan Chibok 18 Da Aka Sace Ga Iyalansu

Zulum ya bai wa ’yan matan tallafin kayan abinci da tsabar kudi Naira miliyan 1.4

Shugaban Karamar Hukumar Chibok a jihar Borno, Umar Ibrahim Hauri ya mika ’yan mata 18 da aka ceto ga iyalansu a karshen mako.

10 daga ciki cikin wadanda ake ceto  ’yan garin Chibok ne, sauran takwas kuma an sace su ne daga Unguwar Pemi ta karamar hukumar.

Hon. Hauri ya ce Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya amince a fitar da kudi Naira miliyan 1.4 da tallafin abinci ga wadanda abin ya shafa ta hannun Ma’aikatar Harkokin Mata da Cigaban Jama’a.

Kowacce daga cikin ’yan matan Chibok 10 ta samu kudi Naira 100,000 da kayan abinci, yayin da sauran takwas da aka sace a unguwar Pemi  aka ba su Naira 50,000, da kayan abinci kowaccensu.

Shugaban, a lokacin da yake gabatar da kayayyakin, ya gode wa Gwamna Zulum bisa tallafin da ya ba su, ya kuma bukaci wadanda suka amfana da su yi amfani da su yadda ya kamata.

Wadanda suka halarci bikin mika kudaden da kayayyakin tallafin sun hada da mataimakin shugaban karamar hulumar, sakataren karamar hukumar, kansiloli, shugabannin gargajiya, masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC, shugabannin mata da dai sauransu.