✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada dan NYSC sabon Hakimin Yantumaki

Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ya nada dan yi wa kasa hidima (NYSC) a matsayin Sabon Hakimin Yantumaki. Ayyana sabon Hakin Yantumakin na zuwa…

Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman ya nada dan yi wa kasa hidima (NYSC) a matsayin Sabon Hakimin Yantumaki.

Ayyana sabon Hakin Yantumakin na zuwa ne bayan rasuwar Marigayi Alhaji Atiku Abubakar Maidabino.

Sabon Hakimin mai suna Atiku Abubakar Atiku, shi ne babban dan marigayin wanda ‘yan bindiga suka kashe a makon jiya.

Sakataren Masarautar Katsina kuma Sallaman Katsina Bello Ifo ya sanar da haka, sannan ya kara da cewa sabon Hakimin ‘yan tukamin na ci gaba da aikin yi wa bauta kasa (NYSC) a halin yanzu.

A makon jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari a garin ‘yan tumaki inda suka shiga gidan marigayin suka bindige shi.

Yantumaki na karkashin Karamar Hukumar Danmusa ne a jihar Katsina.