✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada sabon Firaminista a Sri Lanka

Sabuwar gwamnatin da Ranil Wickremesinghe zai jagoranta tana da jan aikin farfado da tattalin arzikin kasar.

Shugaba Gotabaya Rajapaksa na kasar Sri Lanka ya rantsar da Ranil Wickremesinghe mai shekaru 73 da haihuwa a matsayin sabon firaministan kasar.

Tuni shugaban kasar ya bukaci ’yan adawa da jami’an gwamnatinsa bisa aiki tare kan samar da mafita bisa yanayin da kasar take ciki na matsalolin tattalin arziki.

Sabon firamnistan ya kasance gogaggen dan adawa wanda yake rike mukamun sau biyar, kuma sabuwar gwamnatin da Firaminista Ranil Wickremesinghe zai jagoranta tana da jan aikin farfado da tattalin arzikin kasar.

Nadin ya zo kwanaki uku bayan Firamnista Mahinda Rajapaksa dan-uwan Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya ajiye aiki sakamakon zanga-zanga kan tabarbarewar tattalin arziki da kasar ta Sri Lanka ta samu kanta a ciki.

Tashe-tashen hankula da suka biyo zanga-zangar neman gwamnatin kasar ta yi murabus sun janyo mutuwar mutane tara yayin da wasu kimanin 300 suka jikata.

Aminiya ta ruwaito cewa, Firaminista Mahinda Rajapaksa ya yi murabus ne bayan gagarumar zanga-zanga ta kaure, inda rahotanni sun nuna cewa magoya bayan firamistan dauke da sanduna da kulake, sun kai hari kan masu zanga-zangar.