✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada sabon Kwamishinan ’Yan sanda a Kaduna

Sabon kwamishinan ’yan sandan ya kama aiki nan take.

Abdullahi Mudassiru, ya zama sabon Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kaduna, bayan karin girma da aka yi wa CP Umar Muri.

Kakakin ’yan sandan jihar, Mohammed Jalige, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Kaduna.

  1. Cutar Kwalara ta kashe mutum 816 a Najeriya —NCDC
  2. Jarumar Kannywood, Diamond Zahra ta amarce

Ya ce Mudassiru ya maye gurbin tsohon Kwamishinan ’Yan Sanda a Jihar, Umar Muri wanda aka kara wa girma zuwa Mataimakin Sufeto Janar.

Sabon kwamishinan wanda ya fito daga Jihar Katsina ya yi digirinsa na farko a fannin kimiyyar siyasa a Jami’ar Usmanu Danfodio, da ke Sakkwato.

Ya fara aikin dan sanda a matsayin Mataimakin Sufeton ’yan sanda na bayan kammala Kwalejin Horas da Kananan Hafsoshin ’Yan Sanda da ke Kaduna a ranar 3 ga Maris 1990.

Mudassiru ya yi aiki a fannoni daban-daban daga ciki akwai Jami’in da ke Kula da Rundunar yaki da ’yan fashi a Jihar Abia.

Ya kuma rike mukamin Kwamandan Shiyya ta 1 da ke garin Wudil, a Jihar Kano, Ijebuode Jihar Ogun da Ahoda a Jihar Ribas.