✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An nada sabon Sarkin Dutse

Muhammad Hameem ya zama sabon Sarkin Dutse a Jihar Jigawa.

Masu Zaben sarki na Masarautar Dutse sun yi ittifaki tare da zaben Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse a Jihar Jigawa.

Gwamnan Jihar Jigawa, Abubakar Muhammad Badaru, ya amince da nadinsa daga ranar Lahadi 5 ga watan Fabrairu, 2023, bayan daukacin masu zaben sarkin su bakwai sun jefa masa kuri’unsu, daga cikin mutum uku da suka nemi sarautar.

Sanarwar da msarautar ta fitar ta ce bayan haka ne aka mika sakamakon ga Majalisar Sarakuna ta Jihar Jigawa wadda ita ma ta amince da abin da Masu Zaben Sarkin suka yi.

Daga nan ta mika sunan Muhammad Hameem da sauran mutum biyun da suka tsaya takara ga Gwamna Muhammad Badaru Abubakar domin amincewarsa.

Gwamnan Badaru, ya amince da nadin Muhammad Hameem Nuhu Sanusi a matsayin sabon Sarkin Dutse daga ranar Asabar  5 ga watan Fabrairu, 2023, kamar yaddaga gwamnatin jihar ta sanar.