✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An nada sabon Shugaban Jami’ar Tarayya ta Gusau 

Majalisar Gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS), ta sanar da nadin Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau a matsayin sabon Shugaban jami’ar. Sanarwar ta fito ne daga…

Majalisar Gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Gusau (FUGUS), ta sanar da nadin Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau a matsayin sabon Shugaban jami’ar.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Shugaban Majalisar, Honarabul Yissa Ezekiel Benjamin a babban dakin taro na jami’ar bayan zaman majalisar na musamman karo na 20 da aka gudanar a ranar Alhamis, 10 ga watan Dasumba.

Honarabul Yissa ya bayyana cewa tsarin zabar sabon shugaban jami’ar ya fara ne tun yayin da Jami’ar ta ta tallata bukatar hakan a wasu manyan jaridu biyu na kasar.

Ya ce Farfesa Mu’azu ya zama gwarzo daga cikin bajiman malamai 25 daga jami’o’i daban-daban da suke nemi shugabancin jami’ar bayan cika ka’idodin da aka shar’anta.

Farfesa Mu’azu wanda shi ne cikon Shugaban jami’ar na uku a tarihi, zai yi aiki na wa’adin shekaru biyar a karon farko wanda zai fara daga ranar 10 ga watan Fabrairun 2021.

Aminiya ta ruwaito cewa Farfesa Mu’azu wanda ya fito daga jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sakkwato, kwararre ne a fannin nazarin yanayi da tasirin sunadarai a jikin halittu wato Toxicology kuma ya yi karatun digirin digirgir a Jami’ar Surrey da ke Birtaniya.