Daily Trust Aminiya - An nada sabon Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano
Subscribe

Jami’ar Yusuf Maitama Sule

An nada sabon Shugaban Jami’ar Yusuf Maitama Sule ta Kano

Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke jihar Kano, ta amince da nadin Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa a matsayin sabon Shugaban Jami’ar.

Shugaban Majalisar, Farfesa Muhammad Yahuza Bello, shi ne ya sanar da hakan cikin wata wasikar bayar da tabbaci da ta ce nadin zai fara aiki ne daga ranar Juma’a 16 ga watan Oktoba.

Farfesa Kurawa wanda shi ne Shugaban Poly ta Kano, ya zama gwarzo cikin mutum takwas da suka yi takarar neman shugabancin jam’iyyar ta gwamnatin jihar.

Sabon shugaban zai jagoranci jami’ar daga yanzu har zuwa tsawon shekaru biyar masu zuwa.

Wadanda suka nemi shugabancin jami’ar sun hadar da Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji na jami’ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil; Farfesa Bako El-Yakub Jibril da Farfesa Sadiq Z. Abubakar daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Sauran su ne; Farfesa Ali Tijjani Abdullahi da Farfesa Lawan Alhassan Bichi daga jami’ar Bayero, Shugaban Kwalejin Nazarin Addinin Musulunci da Shari’a ta Aminu Kano, Farfesa Balarabe Jakada, sai kuma Farfesa Aliyu Musa.

More Stories