✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An nada sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati a Sakkwato

Gwamna Aminu Waziri na Jihar Sakkwato, ya nada Mallam Abubakar Muhammad wanda aka fi sani da Dan Shehu a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati a…

Gwamna Aminu Waziri na Jihar Sakkwato, ya nada Mallam Abubakar Muhammad wanda aka fi sani da Dan Shehu a matsayin sabon Shugaban Ma’aikatan Gwamnati a Jihar.

Sanarwar da Gwamnati ta fitar ta bayyana nadin ta ce Dan Shehu zai soma aiki ne nan take.

Wannan nadi ya biyo bayan ritayar da tsohon Shugaban Ma’aikatan,  Alhaji Sani garba Shuni ya yi a yayin da shekarunsa na haihuwa suka cika 60 a ranar 30 ga watan Dasimbar 2020.

Sabon Shugaban Ma’aikatan wanda ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Usman Danfodiyo inda ya karanci nazarin halayyar dan Adam, an haife shi ne a ranar 4 ga watan Fabrairun 1967.

A shekarar 2009, ya halarci makarantar Horas da Manyan Jami’an Gwamnati da ke birnin Jos na Jihar Filato.

Kafin haka ya yi aiki a Kamfanin Jarida na Jihar Sakkwato a shekarar 1992 har zuwa lokacin da ya zama babban Sakatare inda aka mayar da shi Ma’aikatar Gona ta Jihar a shekarar 2008.

Daga bisani ya yi aiki a wurare daban-daban a matsayin babban Sakatare kama daga Hukumar Alhazai ta Jihar, Ma’aikatar yada Labarai da Manyan Makarantu har zuwa Ma’aikatar Lafiya kafin ya samu wannan sabon mukami na yanzu.

Dan Shehu ya taba zama mai taimaka wa Tsohon Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko a sashen yada labarai.