An nada Sanata Ahmad Lawan sarauta a kasar Ibo | Aminiya

An nada Sanata Ahmad Lawan sarauta a kasar Ibo

    Abubakar Muhammad Usman da Abdullateef Salau

An yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan nadin sarauta a kasar Ibo, inda ya yi kira ga jama’ar sassan Najeriya su zauna lafiya da junansu.

An nada Sanata Ahmad Lawan mukamin Babban Cif mai matsayin ‘Nwannedinamba I’ na Igbere, wanda Masarautar Yabi ta Igbere karkashin jagorancin Ndi Eze ta yi a ranar Lahadi a Igbere Ebiri, Jihar Abiya.

Daga cikin wadanda suka halarci nadin sarautar akwai Mai Tsawatarwar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Uzor Kalu, Mataimakinsa, Aliyu Sabi Abdullahi, Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye Sahabi Ya’u, Sanata Sani Musa da kuma Shugaban Ma’aikatan Majalisa, Babagana Aji.

Ahmad Lawan yayin da yake karbar shaidar nadin sarautar

Ahmad Lawan da tawagar da suka raka shi amsar nadin sarautar