An nada Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura | Aminiya

An nada Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura

Yusuf Buhari da mahaifinsa. (Hoto: Bashir Ahmad)
Yusuf Buhari da mahaifinsa. (Hoto: Bashir Ahmad)
    Sagir Kano Saleh

Masarautar Daura ta nada dan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Yusuf a matsayin Talban Daura.

Sarkin Daura ya ba wa Yusuf Buhari sarautar Talban Daura ne a ranar Sallah, kamar yadda mai magana da yawun Shugaban Kasa, Garba Shehu ya sanar.

“Ina tare da Yusuf Buhari, wanda ba da jimawa ba aka ayyana a matsayin Talban Daura da kuma Danmadamin Daura, Musa Daura’ kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya sanya hotonsa da matasan su biyu.

Sarautar Talba, babbar sarauta ce a Masarautar Daura, wadda Sarki Umar Farouq yake jagoranta.

Musa Daura, da ne ga Shugaba Muhammadu Buhari, kuma shi ne Danmadamin masarautar a cewar Garba Shehu.

Tun makon jiya Shugaba Buhari ya je mahaifarsa da ke Daura a Jihar Katsina, inda ya kammadar da wasu ayyuka, yake kuma hutun Sallah.