✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ninka wa ma’aikatan shari’a albashinsu a Kuros Riba

Karin zai fara aiki ne daga watan Yulin 2022

Gwamnan Jihar Kuros Riba, Ben Ayade, ya amince da ninka wa ma’aikatan shari’a na Jihar albashinsu da kudaden alawus-alawus.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Magana da Yawun Gwamnan, Mista Christian Ita ya fitar ranar Talata.

Ya ce Gwamnan ne ya bayyana hakan a bikin rantsar da sabon shugaban kotunan daukaka kara na jihar, Mai Shari’a Anjor Mbe.

Sanarwar ta ce sabon tsarin albashin zai fara aiki ne daga kan ma’aikatan manyan kotunan jihar daga ranar daya ga watan Agustan 2022.

“Su ma ma’aikatan kotun daukaka kara za a ninka musu, yayin da ma’aikatan kotunan majistare za a kara musu rabin albashin nasu,” inji shi.

Kazalika, ya kuma bayyana daukar sabbin ma’aikatan shari’a 500 aiki nan take, a kashi na farko na kara ma’aikatan shari’a da Gwamnatinsa ke yi.

Gwamnan ya kuma ce gwamnatinsa ta amince da ajiye kaso 25 na alawus-alawus din ma’aikatan shari’ar, wadanda suka hada da na tafiya da hutu da sauransu.

Ayade ya yi alkwarin ci gaba da kula da bukatun ma’aikatan bangaren shari’ar a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Haka kuma, ya ce wannan tagomashi ya biyo bayan rahoton da kwamitin kula da walwalar bangaren shari’a na jihar da aka kafa tun a watan Afrilu ya mika masa, wanda ya bayyana halin da ma’aikatan shari’ar ke ciki.