✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An raba wa iyalai 2,435 naman layya a Neja da Nasarawa

Akalla iyalai 2,435 ne suka rabauta da naman layya da wani shirin kasar Kuwait na sadaukar da nama da Babbar Sallah ya yi a jihohin…

Akalla iyalai 2,435 ne suka rabauta da naman layya da wani shirin kasar Kuwait na sadaukar da nama da Babbar Sallah ya yi a jihohin Neja da Nasarawa.

Kimanin shekaru 25 kenan da kasar ke yanka raguna da shanu domin raba wa  talakawa lokacin bukukuwan sallah.

Da yake jawabi lokacin raba naman a Minna, babban birnin jihar Neja, darektan Kungiyar Musulunci ta Bayar da Tallafin Kasa da Kasa a Najeriya, Alhaji Abdulwasie Zubair Adesina ya ce iyalan da suka rabauta da kabakin sun fito ne daga jihohin Neja da Nasarawa.

Adesina ya kara da cewa shirin wanda gidauniyar wakafi ta kasar ta Kuwait ta dauki nauyi a jihohin biyu ya lakume sama da Naira miliyan tara a bana.

Shi ma da yake nasa jawabin, babban darektan hukumar  kula da harkokin addinai ta jihar Neja, Umar Faruk Abdullahi ya yaba wa namijin kokarin da kasar ta Kuwait ta yi na faranta ran talakawa, marayu da masu karamin karfin da basu da ikon yin layya a jihar ranar Sallah da tallafin naman.

Ya kuma yi fatan cewa shirin zai dore domin yunkurin ya dace da na gwamnatin jihar na ganin ta dadada wa marasa karfi.

Babban darektan ya kuma ce ita ma gwamnatin jihar ta kashe kimanin Naira miliyan 30 wajen rabon raguna da sauran kayan abinci ga malamai, limamai da sauran jama’a lokacin sallar ta bana.