✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

HOTUNA: An raba wa ’yan kasuwar Kantin kwari tallafin Atiku na N50m

An raba kudin ne ga mutum 397 a gidan Shekarau

An raba wa ‘yan kasuwar Kantin Kwari su kimanin 397 wadanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa tallafin kudin da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya bayar.

A watan da ya gabata ne dai Atikun ya sanar da bayar da tallafin na Naira miliyan 50 ga ‘yan kasuwar, lokacin da ya je bikin karbar Sanatan Kano ta Tsakiya, Ibrahim Shekarau.

An dai gudanar da rabon kudin ne a gidan Sanatan kuma tsohon Gwamnan Kano da ke unguwar Mundubawa a cikin birnin Kano a ranar Litinin.

Ga wasu daga cikin hotunan: