✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rada wa jaririn Aghanistan da aka haifa a jirgin Amurka sunan jirgin

An dai haifi jaririn ne a sansanin sojojin Amurka na Ramstein a kasar Jamus.

Wani jariri da aka haifa a cikin jirgin sojin Amurka yayin kokarin tserewa daga kasar Afghanistan bayan Taliban ta karbi mulki an rada masa sunan jirgin na Amurka.

An dai haifi jaririn ne a sansanin sojojin Amurka na Ramstein a kasar Jamus, kuma aka rada masa sunan ‘Reach’, kamar yadda kwamandan sojojin Amurkan na kasashen Turai, Tod Walters ya tabbatar yayin wani jawabi ga ’yan jarida ranar Laraba.

Jirgin dai, kirar Boeing C-17 da sojojin suka yi amfani da shi ake yi wa lakabi da Reach.

A karshen mako ne dai rundunar sojin ta Amurka ta wallafa a shafinta na Twitter cewa nakuda ta kama wata mata a kan jirgin da ya taso daga Qatar zai tafi Jamus.

Sai dai ta sami sauki ne bayan ya sauka da nufin ya-da-zango, lamarin da ya taimaka wajen ceto rayuwarta.

A lokacin dai, sojoji sun taimaka wa matar ta haihu a bangaren zuba kaya na cikin jirgin, kamar yadda rundunar ta tabbatar.

“Kamar yadda za ku yi zato, a matsayina na matukin jirgin yaki, burina shi ne na ga wannann jaririn ya girma, ya zama Ba’amurike, sannan ya tuka jirgin yakin kasar a matsayin soja wata rana,” inji Tod Wolters.

Ana dai amfani da sansanin sojin na kasar Jamus a matsayin wani wajen ya-da-zango ga mutanen da aka kwaso daga kasar Afghanistan.

Yanzu haka dai a kan wuce da mutanen da aka kwaso zuwa filin jrigin saman Dulles da ke kusa da birnin Washington kafin daga bisani a rarraba su zuwa wasu sansanoni da ke kasar ta Amurka.

Sansanin dai na Ramstein wanda ke kusa da birnin Kaiserslautern na kasar Jamus shi ne sansani mafi girma da Amurka take da shi a wajen kasarta. (NAN)