✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rage ranakun aikin gwamnati zuwa kwana 4 a Kaduna

Ranar 1 ga Disamba, 2021 ma'aikatan gwamnatin Kaduna za su koma zuwa aikin kwana hudu a kowane mako.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta rage yawan ranakun zuwa aikin ma’aikatanta zuwa kwana hudu a kowane mako.

Gwamnatin ta ce a sabon tsarin, ma’aikata ba za su rika zuwa aiki ranar Juma’a ba, a yunkurinta na kara wa ma’aikata kwazon aiki da karin lokacin zama da iyalansu, tare da fata hakan zai ba su damar rungumar harkar noma.

A karkashin sabon tsarin, “Lokacin aiki zai koma karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma, daga Litinin zuwa Juma’a. Ranar Juma’a, dukkannin ma’aikata za su yi aiki ne daga gida, amma banda malaman makarantu da ma’aikatan lafiya,” inji sanarwar da gwamnatin ta fitar.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce tsarin zai fara aiki ne daga ranar Laraba 1 ga watan Disamba, 2021.

“Za a ci gaba da wannan tsarin a matsayin wucin gadi, kafin daga a kammala tsare-tsaren mayar da ranakun aiki kwana hudu a mako a daukacin hukumomi da ma’aikatin gwamnatin jihar,” inji ta.

Sanarwar da da kakakin gwamnan, Muyiwa Adekeye ta ce, za a koma bin sabon tsarin ne bayan darasin da gwamnatin jihar ta dauka daga matakan dakile cutar COVID-19, da ke bukatar tsarin aiki na zamani ta yadda ma’aikata za su iya yin aiki daga ko’ina.

Ya ce gwamnatin jihar za ta kara kaimi wajen samar wa ma’aikatanta kayan aiki da sauran abubuwan da ake bukata na zamani domin su samu damar yin aiki yadda ya kamata daga gidajensu.

A cewarsa, za a kammala kudurin dokar rage ranakun aiki zuwa kwana hudu a watan Janairun 2022, domin ba wa masu ruwa da tsaki damar ba da shawarwari su kuma rungumi tsarin.