✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da Adesina Shugaban Bankin Afirka a karo na biyu

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) Akinwunmi Adesina ya karbi rantsuwar fara aiki a karo na biyu a wani biki da ya gudana ta fasahar…

Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) Akinwunmi Adesina ya karbi rantsuwar fara aiki a karo na biyu a wani biki da ya gudana ta fasahar bidiyo ranar Talata.

Shugabar Majalisar Gwamnonin bankin kuma ministar kasar Ghana, Kenneth Ofori-Attah ce ta jagoranci rantsuwar.

Mista Adesina wanda tsohon ministan harkokin noma ne a Najeriya ya samu sake darewa kujerar ne bayan ya lashe zaben da aka gudanar ranar 27 ga watan Agusta ba tare da hamayya ba kuma zai shafe karin shakararu a sabon wa’adin.

Kwararre a kan harkokin tattalin arziki, shugaban ya zama jagoran bankin ne ranar 28 ga watan Mayun 2015, kuma shi ne dan Najeriya na farko da ya rike mukamin.

Masana harkar tattalin arziki da dama dai na ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasashen yankin a wa’adin mulkinsa na farko.

Kazalika, kafin a sake zaben nasa a karo na biyu ya fuskanci kalubale iri-iri da suka shafi zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Bankin AfDB dai shi ne babban bankin hada-hadar kasuwanci da ya kunshi kasashen nahiyar 54 da ma wadanda ba na nahiyar ba guda 27.