✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da kwamitin binciken Mataimakin Gwamnan Zamfara

Majalisar Dokokin Jihar ta amince a tsige Mahdi Aliyu Gusau zargin sa da rashin da’a.

Babbar Alkaliyar Jihar Zamfara, Mai Shari’a Kulu Aliyu ta rantsar da kwamatin mutum biyar da zai binciki laifukan da ake zargin Mataimakin Gwamna Mahdi Aliyu Gusau na rashin biyayya.

Kwamatin karkashin tsohon Alkali Tanko Soba, an kafa shi ne sakamakon damar da kundin tsarin mulki ya ba wa alƙaliyar, a cewar Mai Shari’a Kulu.

A cewarta, Sashe na 185(5) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ne ya ba ta damar kafa kwamatin sakamakon buƙatar da Majalisar Dokokin Zamfara ta gabatar mata ranar 10 ga watan Fabarairu ta korafi kan mataimakin gwamnan.

A gefe guda kuma, Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja, ta saka ranar 10 ga watan Maris don fara sauraron karar da Mahdi Gusau ya shigar yana neman kotun ta dakatar da yunkurin tsige shi da ’yan majalisar ke yi.

Aminiya ta ruwaito cewa Mai Shari’a Inyang Ekwo ne ya dage zaman a ranar Talata, yana mai umartar bangarorin su kimtsa kafin ranar ci gaba da shari’ar.

A ranar Alhamis da ta gabata ce ’yan majalisar 18 cikin 22 suka amince a tsige mataimakin gwamnan wanda har yanzu yake a jam’iyyar adawa ta PDP sakamakon zargin sa da rashin da’a.

A bara ce Gwamna Bello Matawalle ya sauya sheka daga PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya inda shi kuwa Mahdi Gusau ya noke a jami’yyar PDP