✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da mace ta farko a matsayin Shugabar Kasar Tanzania

Hakan dai na nufin ita kadai ce za ta kasance Shugabar Kasa mace a nahiyar Afirka, in banda takwararta ta Habasha

A kasar Tanzaniya, an rantsar da Samia Saluhu ranar Juma’a a matsayin Shugabar Kasa, lamarin da ya mayar da ita mace ta farko da ta rike mukamin a kasar.

Hakan dai na zuwa ne bayan rasuwar Shugaba John Magufuli bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Mai kimanin shekaru 61 a duniya, Samia wacce musulma ce, ta fito ne daga yankin Zanzibar kuma za ta kammala wa’adin mulkin tsohon shugaban na shekaru biyar wanda zai kare a 2025.

Sanye da jan mayafi, an rantsar da ita a matsayin Shugabar Kasar ta shida a wani biki da ya gudana a birnin Darissalam kafin kuma daga bisani ta duba faretin da sojoji suka yi mata.

Lokacin da sabuwar Shugabar Kasar take duba faretin sojoji jim kadan da rantsar da ita

Hakan dai na nufin ita kadai ce za ta kasance Shugabar Kasa mace a nahiyar Afirka, in banda takwararta ta Habasha, Sahle-Work Zewde wacce ita ta jeka-na-yi-ka ce.

Mutane da dama dai a wajen kasar ta Tanzaniya ba su san sabuwar Shugabar ba har sai ranar Larabar da ta gabata inda ta bayyana a gidan talabijin domin sanar da rasuwar Magafuli.

Tsohon shugaban dai ya rasu ne yana da shekaru 61 a duniya bayan ya yi fama da ciwon zuciya wanda ya hana shi fitowa cikin mutane kusan tsawon makonni uku.