✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da mace ta farko alkalin alkalan jihar Nasarawa

Aisha Bashir Aliyu, ita ce mace ta farko da ta zama alkalin alkalan jihar.

A ranar Alhamis, Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ya rantsar da Aisha Bashir Aliyu, mace ta farko a matsayin alkalin alkalan jihar.

Nadin nata ya zo ne bayan ritayar alkalin alkalan jihar, Mai Shari’a Suleiman Dikko a ranar 31 ga Disamba, yana da shekaru 65 a duniya.

“Kamar yadda Kundin Dokokin Jihar Nasarawa karkashin sashe na 271 (1), na ba da umarnin rantsar da Aisha Bashir Aliyu, a matsayin alkalin alkalan jihar Nasarawa ta rikon kwarya,” cewar Gwamna Sule.

Yayin rantsar da ita, Gwamnan ya umarce ta da ta yi aikinta yadda ya kamata, kamar yadda jajircewarta ta nuna.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan harkar da ta shafi shari’a a jihar.

Da take nata jawabin, sabuwar alkalin alkalan jihar, ta godewa gwamnan da kuma hukumar gudanarwar ma’aikatar shari’a bisa nadin da aka yi mata.

Ta kara da cewa za ta yi aikinta, cikin tsoron Allah da kuma kawo daidaito ta yadda harkokin shari’a za su samu ci gaba a jihar.

Aisha Bashir Aliyu, ta ce a karkashin jagorancinta, za ta taimakawa gwamnatin jihar wajen gudanar da ayyukanta yadda suka dace.