✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da sabon Sarki a Kuwait

Kwana daya bayan rasuwar Sarkin Kuwait, Sheikh Sabah al-Ahmed al-Sabah, Majalisar Zartarwa ta Kasar ta nada Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah a matsayin sabon sarki da…

Kwana daya bayan rasuwar Sarkin Kuwait, Sheikh Sabah al-Ahmed al-Sabah, Majalisar Zartarwa ta Kasar ta nada Sheikh Nawaf al-Ahmad Al-Sabah a matsayin sabon sarki da har ya karbi ranstuwar kama aiki.

Dama dai an sa ran Sheikh Nawaf wanda shi ne yarima mai jiran gado kuma kanin Marigayi Sheikh Sabah da suke uba daya, ya maye gurbinsa.

Sheikh Nawaf mai shekaru 83 a duniya, ya sha alwashin yin aiki domin samar da daidaito da tabbatar da tsaro a Kuwait.

Wani rahoto da jaridar BBC ta wallafa, ya ce ba a tsammanin Sheikh Nawaf mai shekara 83 zai kawar da kasar daga manufofin cikin gida da na kasashen duniya da magabacinsa ya samar.