✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da sabon Shugaban Kasa a Somaliya

Bikin ya sami halartar Shugabannin kasashe da dama

An rantsar da Hassan Sheikh Mohamud a matsayin sabon Shugaban Kasar Somaliya a ranar Alhamis, a Mogadishu, babban birnin kasar.

Bikin rantsuwar dai ya samu halartar Shugabannin kasashe da dama musamman na Afirka da jakadun kasashen waje.

Daga cikin wadanda suka halarci bikin akwai Shugaban Kenya, Uhuru Kenyatta da Firaministan Habasha, Abiy Ahmed da Shugaban Djibouti, Ismail Omar Guelleh da Firaministan Masar Kamal Madbouly da kuma wakilai daga kasashe Turkiyya da Uganda da Hadaddiyar Daular Larabawa da wasu kasashen Yamma.

Da yake jawabi jim kadan da rantsar da shi, sabon Shugaban ya sha alwashin cewa kasarsa ba za ta rika tsoma baki a kowacce irin siyasar duniya ba, inda za ta zauna a matsayin ’yar-ba-ruwanmu.

Shugaba Hassan ya kuma roki tallafi daga kasashen duniya a daidai lokacin da kasar shi ke fuskantar annobar fari mafi muni a cikin sama da shekara 40.

Su ma da suke jawabi a wajen rantsuwar, Shugaban Kenya da Firaministan Habasha, sun yaba da yadda aka samu sauyin gwamnati cikin kwanciyar hankali a kasar, inda suka yi alkawarin yin aiki da gwamnatin.