✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da shugaban rikon kasar Sri Lanka

Ranar Talata za a gabata wa Majalisar Dokokin sunayen da za ta zabi shugaban kasa daga ciki

Majalisar Dokokin Kasar Sri Lanka ta sanar cewa shugaban rikon kasar ya karbi rantsuwar kama aiki, har zuwa lokacin da za a zabi sabon shugaban kasa.

Shugaban Majalisar Dokokin Sri Lanka, Mahinda Yapa Abeywardana, ya tabbatar da rantsar da Fira Minista Wickremesinghe a matsayin shugaban riko, bayan samun wasikar murabus din da tsohon Shugaba Gotabaya Rajapaksa ya aiko wa majalisar.

“Na sami takardar ajiye aikin shugaban kasa kuma daga yanzu za mu shiga aikin nada sabo,” inji Abeywardana a ranar Juma’a.

Tun da farko, Mista Rajapaksa ya tura wa Majalisar wasikar murabus dinsa ta email, kafin daga bisani a kawo mata kwafi daga kasar Singapore, inda ya koma.

Shugaban Majalisar ya ce zauren majalisar ya amince da murabus din Mista Rajapaksa bayan tabbatar da sahihancin wasikar da ya aiko ranar Alhamis.

Ofishin Shugaban Majalisar ya ce a ranar Talata za a gabatar wa Majalisar Dokokin kasar sunayen ’yan majalisar da za ta zabi shugaban kasar daga cikin, washegari kuma, ’yan majalisar su kada kuri’a.

Ofishin ya bayyana cewa aikin nada sabon shugaba kasar zai dauki tsawon kwana bakwai.

A ranar Laraba tsohon shugaba Gotabaya Rajapaksa ya tsere daga Sri Lanka bayan masu zanga-zanga sun mamaye fadar gwamnatinsa tare neman ya yi murabus saboda gazawa wajen magance matsalolin tsadar rayuwa da durkushewar tattalin arziki mafi muni a kasar.

Da farko ya fara zuwa kasar Maldives ne kafin daga bisani ya koma Singapore a ranar Alhamis.

Jim kadan bayan isarsa Singapore ne ya aike da wasikar ta ajiye aikinsa, duk da cewa da farko ya sanar cewa ranar Laraba, 13 ga watan Yuli da muke ciki zai sauka daga kujerar tasa.