✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rataye ’yan kungiyar ISIS a Iraqi

An zartar musu da hukuncin ne a Gidan Yarin Nasiriyah ranar Litinin.

An zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya a kan wasu ’yan kungiyar ISIS a kasar Iraqi.

Hukumomin lafiya a Iraqi sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutum shida ne aka rataye a ranar Litinin kuma uku daga cikinsu an kama su ne da laifin ta’addanci.

Majiyoyin sun ce an rataye mutanen ne a Gidan Yarin Nasiriyah, inda ake tsare da su a matsayin fursunonin kafin a zartar musu da hukuncin.

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce a shekarar da ta gabata, an zartar da hukuncin kisa a kan mutum 45 a kasar ta Iraqi.

Amnesty ta ce akasarin wadanda aka kashe din a bara an zartar musu da hukuncin ne a kan laifin zama ’yan kungiyar ISIS.