✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe babbar kasuwar Abuja saboda karya dokar COVID-19

Wakilinmu ya ga yadda wasu daga cikin ’yan kasuwar sun yi zaman dirshan a kofofin shigarta.

Wani ayarin jami’an tsaro ya kai samame babbar kasuwar Abuja dake Wuse a ranar Talata inda suka garkameta saboda zargin karya dokar kariyar COVID-19.

Wakilinmu da ya isa wajen da misalin karfe 12 na ranar Talatar, ya ga yadda wasu daga cikin ’yan kasuwar suka yi zaman dirshan a biyu daga cikin kofofin shigarta.

Rahotanni sun nuna cewa gabanin daukan matakin, an ga kwamitin da Ministan Abuja Malam Muhammad Musa Bello ya kafa don tabbatar da bin dokar a yankin Babban Birnin Tarayya a qarqashin jagorancin Mista Attah Ikharo, ya kai ziyarar gani da ido kasuwar a ranar Litinin.

Wani daga cikin ’yan kasuwar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya zargi wasu daga cikin abokan zamansu a kasuwar da jawo masu daukar matakin kan kin amfani da takunkumin.

Ya ce “Abin mamaki ne musamman ga wanda ya san akwai cuta da magani akwai hukuma, sannan a saka masa doka ya ki bi.

“Hakan na faruwa ne duk da suna da masaniyar cewa a akwai yuwuwar a dauki mataki mai tsauri a kan hakan,” inji shi.

Wani daga cikin ’yan kasuwan mai suna Musa Faruku da ya kasance a cikin gungun masu zaman jiran tsammani a wajen kasuwar, inda ya ce lamarin ya zo masu da ba-zata kasancewar an rufe kasuwar tun gabanin lokacin budeta.

Ya ce a yadda ya saba ya kan bar cinikinsa ne da katin cirar kudi na ATM a shagonsa da ke cikin kasuwar don gudun matsalar hanya a yayin komawa gida da daddare.

“A yanzu ban san yadda zan sami kudin da za su mayar da ni gida ba, ballantana sauran kudaden yau da kullum,” inji shi.

Ya kara da cewa a yayin da kwamitin ministan ya kai ziyarar, an kama kamar mutum 60 a tsakanin ’yan kasuwar da masu zuwa sayayya wajen, don a zartar masu da hukuncin tarar Naira 10,000 ko zaman kurkuku na watanni shida.

Wakilinmu ya rawaito cewa bankuna da sauran manyan kantina da ke kewaye da kasuwar sun ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Bayanai sun nuna cewa kasuwar za ta cigaba da kasancewa a rufe har tsawon kwanaaki uku a matsayin gargadi.

Kazalika, dole a tanadi kayan wanke hannu a bakin kowanne shago, baya ga tabbatar da cewa jama’a na sanya takunkumi a fuskokinsu.