✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

#EndSARS: An rufe Babbar Kotun Tarayya

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta kasance a rufe yayin da zanga-zangar #EndSARS ke ci gaba a fadin Najeriya. Wani jami’in tsaro…

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta kasance a rufe yayin da zanga-zangar #EndSARS ke ci gaba a fadin Najeriya.

Wani jami’in tsaro a kotun ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) cewa ba a bude kotun ba don aiki a ranar Alhamis.

Ba a bari masu shigar da kara da sauran mutane sun shiga harabar kotun ba saboda an umarci alkalai da ma’aikata su rufe ayyuka a ranar Laraba.

Zanga-zangar #EndSARS da ake yi a Najeriya kan cin zalin ’yan sanda ya sa wadanda ke kusa da kotun hanzarta barin wurin.

Idan ba a manta ba, a ranar Laraba, wasu ’yan daba sun kai hari kan wasu gine-gine tare da kona wasu, ciki har da Babbar Kotun a Jihar Legas.