✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe coci mai shekara 220 saboda karancin masu ibada

Cocin dai ya kafa tarihin yin ibadarsa ta karshe kafin a rufe shi.

Wani coci mai shekara 221 a Jihar Pennsylbania da ke Amurka ya shiga tarihi bayan da ya gudanar da ibadarsa ta karshe kafin a rufe shi, saboda karancin masu zuwa ibada.

Cocin wanda ake kira da Presbyterian yana Gundumar Bellefonte, shi ne coci mafi tsufa a gundumar, ya gudanar da ibadarsa ta karshe ce a jajiberin Kirsimeti bayan da ya yi maraba da wadansu iyalan da suka taba halartar cocin da ya shafe sama da karni biyu.

“Akwai alamar kauna a cikin wannan Ikilisiyar. Dukkanmu mun san juna tunda dadewa kuma mun san abubuwan da suke faruwa a junanmu,” inji Shugabar Cocin, Rabaran Candace Dannaker kamar yadda jaridar Daily Times ta ruwaito.

“Zan rasa wasu halayen mahalarta, dariyarmu da farin cikinmu suna kasancewa tare. Kuma ba shakka, fannin bangaskiya na raba hakan tare da sauran mutane masu tunani iri daya,” inji ta.

An kafa cocin ne a shekarun 1800 mutanen da suka kafa shi mazauna Gundumar Bellefonte sun gina shi ne a 1795 a lokacin da jihohi 16 ne kawai aka kidaya a cikin mambobinsa tsofaffin gwamnonin Jihar Pennsylbania biyu suna cikinsa.

Mahalarta cocin suna haduwa a harabar cocin kusan shekara 20 a wani ginin dutse. An gina shi ne jim kadan bayan Yakin Basasar Amurka.

Rabaran Dannaker ta ce cocin yana da mambobi 40 kafin barkewar annobar Kwarona, amma adadin ya ragu zuwa 25, kuma babu wanda ya halarci cocin don ibada tun guda daga watan Maris 2020 zuwa ranar Ista.

Lokacin da Dannaker ta fara jagorantar cocin a shekara 34 da suka gabata ta ce, akwai mutane kusan 200 da suke halartar cocin.

Wata mamba a cocin mai suna Pam Benson, mai shekara 77, ta zama mamba ce a tsawon shekara 73.

Ta ce lokacin da aka haife ta a lokacin Yakin Duniya na Biyu, ana rufe kasuwanni da yawa a ranar Lahadi kuma ana shirya wasu abubuwa kadan.

Ta kuma yi imani cewa, iyaye kadan ne suke dagewa kan ’ya’yansu su halarci cocin kuma ba a koyaushe mambobin ke yunkurin daukar sababbin mambobi masu gadanarwa ba.

“Ya bambanta sosai. Abin da kuka yi ne kawai. Sai dai idan ba ku da lafiya sosai, abin da kuka yi ne kawai,” inji Benson.

“Sauyi ne kawai, ci gaba ne. Abin da ya faru ke nan. Ba wai ina son sa ba, amma shi ne abin da yake faruwa,” inji ta.

An shirya za a rufe cocin mai fadin murabba’in kafa dubu 15, a karo na karshe a yau Juma’a 31 ga Disamba.

Kuma Misis Dannaker ta ce, ba a tantance makomar ginin cocin ba.

An wallafa bidiyo na ibadar karshe da aka yi a shafin Facebook na cocin, wadda ta hada da nasihohi game da “takaicin ban-kwana da juna.”

Tare da tunatarwa cewa, “kalubale ba wani sabon abu ba ne ga dan Adam” da kuma wallafa sakon Kirsimeti na bege, da ya dace da wannan lokaci kuma yana da muhimmanci a yau kamar yadda yake a shekara 200 da suka gabata.”

Kafin wakar karshe, mambobin cocin sun kunna kyandir suka daga shi sama tare da fadin: “Haske yana wargaza duhu. Kuma fatar tamu ce sau daya kuma ta karshe.

“Kuma wannan hasken yana kiranmu gaba, yana tunawa da abin da ya gabata, da tafiya cikin aminci zuwa gaba. Yanzu kuma ku tafi cikin salama ta ruhin Kiristi.”