✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe FCE Yola saboda boren dalibai kan rashin ruwa

Dalibai na zargin hukumar makarantar da rashin gyara musu ruwa.

An rufe Kwalejin Ilimi ta Tarayya (FCE) da ke Yola, Jihar Adamawa, bayan zanga-zangar da dalibai suka gudanar saboda rashin ruwa.

Hukumar gudanarwar FCE Yola ta ba da umarnin rufe makarantar ce a ranar Talata, bayan zanga-zangar daliban ta tsayar da harkoki cik.

A safiyar Talata daliban suka fara gudanar da zanga-zangar, saboda rashin ruwan da suka ce ya addabe su, suna kuma zargin hukumar makarantar da rashin yin katabus domin magancewa.

Aminiya ta gano cewa hukumar makarantar ta dauki matakin rufe ta ne saboda guje wa abin da zai je, ya dawo, na karya doka da oda.

Magatakardar FCE Yola, Ahmad Gidado, ya shaida wa manema labarai a ofishinsa cewa lalacewar babbar rijiyar burtsatsen zamanin da ke samar wa daukacin kwalejin ruwa, ita ce ta haifar da matsalar rashin ruwan.

A cewarsa, tun ranar Litinin da hukumar makarantar ta samu labarin matsalar, ta dauki matakan gyara, amma abin takaici sai aka wayi gari ranar Talata daliban suna bore.