✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe kasuwa saboda rashin bin ka’idar COVID-19

Za a sake rufe kasuwa bayan kwana 10 da budewa saboda saba ka’idojin hana yaduwar cutar COVID-19 a jihar Anambra. Gwamnatin jihar za ta rufe…

Za a sake rufe kasuwa bayan kwana 10 da budewa saboda saba ka’idojin hana yaduwar cutar COVID-19 a jihar Anambra.

Gwamnatin jihar za ta rufe kasuwar Awka daga ranar Litinin 15 ga watan da muke ciki saboda ‘yan tireda da sauran ‘yan kasuwa da dillalai sun karya sokar.

Sanarwar da Kwamishinan Yada Labaran Jihar, C. Adinu ya fitar ranar Alhamis ta ce, “Sakamakon haka Gwamnatin Jihar Anambra za ta sake rufe Kasuwar Awka na tsawon mako biyu daga ranar 15 ga Yuni, 2020.

Da take sanar da bude kasuwanni bayan makonni biyar da rufe su domin hana yaduwar cutar, gwamnatin jihar ta shardanta wa amfani da kyallen rufe fuska da samar da kayan wanke hannu a kowane layi a kasuwanni.

Haka kuma dole ne a rika wanke hannu akai-akai tare da bayar da tazarar taku shida tsakanin mutane.

Kwamishinan ya nuna damuwa kan yadda ya ce an yi watsi da matakan, musammanma a kasuwar ta Awka.

Adinuba  ya ce karin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 da wadanda ta kashe a jihar ya nuna alkaluman sun fi karuwa ne a karamar hukumar da kasuwar take —Awka ta Kudu.
“Gwamnati na lura da yadda ake bin ka’idojin a kasuwanni kuma za ta rufe duk kasuwar da ta saba dokokin nan take har sai abin da hali yayi”, inji Kwamishinan.
Sanarwar ta kuma umarci dukkan wurare da mutane ke taruwa a jihar da su tabbata ana bin ka’idojin dakile COVID-19 sau da kafa.
Ta kuma ce gwamnatin jihar za ta kafa kotunan tafi-da-gidanka domin cin tarar masu saba dokar N10,000  ko sa su yi aikin taimakon al’umma.