✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe Kasuwar Dei-dei kan rikicin ’yan acaba da ’yan kasuwa

An yi asarar rayuka da dukiyar akalla Naira biliyan daya, ciki har da shaguna 45

Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Bello, ya rufe Babbar Kasuwar Dei-dei bayan rikicin da ya barke tsakan ’yan kasuwa da ’yan acaba a ranar Laraba.

Ya ba da umarnin ne bayan ya jagoranci jami’an gwamanti da hukumomin tsaro ziyarar gani da ido a yankin da rikicin ya auku don gane barnar da aka tafka.

Ministan ya ce, “An rufe kasuwar da kuma dakatar da hada-hadar kasuwanci a bakin hanya da suka takure hanya har sai hukuma ta kammala bincike kafin daukar mataki na gaba.”

Shaguna 45 zuwa 50 ne suka kone a kasuwar sakamakon rikicin da ya yi lalata dukiya ta sama da Naira biliyan daya, kamar yadda Mataimakin Shugaban Kasuwar, Ifeanyi Chibata, ya shaida wa Ministan Abuja.

Bayanai sun nuna rikicin ya samo asali ne bayan da wata ’yar kasuwar ta fado daga kan babur din haya, wata babbar mota ta bi ta kanta ta yi ajalinta.

Ministan ya umarci shugabannin kasuwar su bincika su gano bata-garin da ke da hannu a rikicin.

“Dole ne mazauna yankin da ma shugabannin kasuwar su gano bata-garin da suka haddasa rikicin.

“Abin takaici ne yadda bata-garin suka yi amfani da bindiga wajen harbin mutane da ba su jib a, ba su gani ba.

“Ni kaina ga gawarwaki guda hudu, wannan ba daidai ba ne, kuma hukumar Abuja ba za ta lamunci hakan ba,” inji shi.

Ya kara da cewa, “Jami’an tsaro su zurfafa bincike, kuma dole ne al’ummar yankin su ba da gudunmawarsu wajen hana aukuwar hakan a gaba, in ba haka ba, ba za a samu zaman lafiya ba.”

Daga nan sai ministan ya yi kira ga al’ummar Abuja da su sani cewa rikicin bai shafi addini ko kabila ba, saboda mazauna yankin da lamarin ya shafa an san su da zaman lafiya a tsakaninsu.